Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu zata gurfanar da ‘Yan tawaye a Kotu

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu tace zata gurfanar da shugabannin ‘Yan tawaye a kotu akan zargin yunkurin kifar da gwamnatin kasar, a wani mataki da ake ganin zai gurgunta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Juba da ‘Yan tawayen.

Riek Machar da Salva Kiir da ke fada da juna a kasar Sudan ta Kudu
Riek Machar da Salva Kiir da ke fada da juna a kasar Sudan ta Kudu REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Yanzu haka akwai yankunan da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan tawaye bayan bangarorin biyu sun amince da matakin tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Ministan shari’a Paulino Wanawila yace zasu gurfanar da shugabannin ‘Yan tawayen da ake tsare dasu guda uku hadi da shugabansu Riek Machar da wakilinsu Taban Deng wanda ya sa hannu ga yarjejeniyar tsagaita wuta.

A ranar 15 ga watan Disemba ne Shugaba Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa a Juba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.