Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Ana ci gaba da rikici a Sudan ta Kudu

Kasashen Duniya sun bayyana fargaba game da rikicin Sudan ta Kudu tare da yin matsin lamba ga bangarorin da ke rikici su rungumi matakan tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin kasar.

Dakarun Sojin gwamnatin Sudan ta kudu da ke yaki da dakarun Machar
Dakarun Sojin gwamnatin Sudan ta kudu da ke yaki da dakarun Machar AFP PHOTO/Charles LOMODONG
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa akan barazanar da dakarun Sudan ta kudu ke yi wa Jami’anta a sansanin da mutane suka tsere wa rikicin.

Dubban mutane aka kashe a Sudan ta kudu yayin da Miliyoya suka gujewa gidajensu domin tsira daga rikicin kasar tsakanin dakarun sojin shugaba Salva Kiir da dakarun ‘Yan tawaye da ke biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Akwai yunkuri da kasashen gabacin Afrika suka yi na sasnata bangarorin biyu wadanda majalisar Dinkin Duniya ta zarga sun aikata laifukan yaki da suka hada kisa da fyade. Amma Shugaba Salva Kiir ya yi watsi da zargin tare da kare gwamnatinsa da ke fuskantar bazarana.

Yanzu haka dai an soke taron gaggawa da aka shirya gudanarwa a gobe Alhamis a Juba wanda masu shiga tsakanin rikicin kasar na kungiyar gabacin Afrika suka nemi su gana da wakilan bangaorirn da ke rikici domin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Rikicin kasar yanzu ya rikide ne zuwa na kabilanci tsakanin kabilan Dinka ta salva Kiir da kuma kabilar Machar inda suke ci gaba da gwabza fada a yankunan kasar masu arzikin fetir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.