Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Ana bi gida–gida domin cafke magoya bayan Machar a sudan ta kudu

Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka sojin gwamnatin Sudan ta Kudu suna shiga gida-gida domin cafke wadanda ake zargin cewa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ne Riek Machar a garin Malakal wanda sojan na gwamnati suka kwace.

Dakarun Sojin gwamnatin Sudan ta kudu da ke yaki da dakarun Machar
Dakarun Sojin gwamnatin Sudan ta kudu da ke yaki da dakarun Machar REUTERS/James Akena
Talla

Vanina Maestracci, daya daga cikin masu magana da yawun Majalisar ta ce jama’a da dama ne ake gallazawa a irin wannan samame da dakarun Salva Kiir suka kaddamar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen yankin gabashin Afirka suka bayyana aniyarsu ta aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar.

Kungiyoyin agaji sun ce sama da mutane 10,000 aka kashe tun barkwar rikicin Sudan ta kudu a ranar 15 ga watan Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.