Nijar
Za’a binciki Tandja da Djibo game da dukiyar kasa a Nijar
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tace zata gudanar da bincike akan ikirarin da tsohon shugaban kasar Mamadu Tandja ya yi na cewa ya bar kudi CFA Miliyan dubu dari hudu a asusun kasar kafin Sojoji su kifar da gwamnatinsa a shekara ta 2010.
Wallafawa ranar:
Talla
Ministan shari’a sannan kuma kakakin gwamnatin Kasar Morou Amadou ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, inda yace shugaba Tandja da kuma wanda ya kifar da shi Janar Salou Djibo dukkaninsu zasu bayyana a gaban kwamitin bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu