Isa ga babban shafi
Najeriya

Ban Ki-moon ya bukaci Najeriya ta sake nazarin dokar auren jinsi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sake nazari a kan dokar haramta auran jinsi guda tare da haramta ayyukan luwadi da madigo, Ban yace dokar na iya haifar da tashin hankali a kasar.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon REUTERS/Kacper Pempel
Talla

Kakakin Sakataren Martin Nesirky, yace Ban na fatar ganin an sauya dokar.

Karkashin sabuwar dokar ta Najeriya, duk jinsi guda da aka kama suna mu’amula ko kokarin yin aure zasu fuskanci hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Tuni dai dokar ta fara aiki inda a garin Bauchi aka cafke wasu mutane guda biyar da suka samar da wata kungiyar neman Maza.

Rahotanni sun ce akwai mutane da dama da aka cafke a biranen Ibadan da Owerri da Awka.

Najeriya dai yanzu ta shiga sahun kasashe 78 da suka la’anci auren jinsi guda, inda a wasu jahohin arewacin kasar hukuncin kisa ne ya hau kan duk wadanda aka kama suna luwadi karkashin dokar shari’ar Musulunci.

Tuni dai Hukumar Hisba a Jihar Kano ta yi na’am da wannan matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.