Isa ga babban shafi
Nigeria

EU ta yi Allah wadai da dokar hana auren jinsi Daya a Nigeria

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ta yi Allah wadai da matakin da Najeriya ta dauka na haramta auren jinsi daya.A cewar Ministar harkokin wajen kungiyar, Catherine Ashton, kungiyar ba ta goyon bayan nuna wariya akan jinsi, ta na mai cewa hakan ya sabawa hakkin bil adama.A ranar litinin ne Shugaban Goodluck Jonathan ya saka hanu akan dokar, kusan watanni uku bayan da Majalisar dokokin kasar ta amince da ita.Yanzu dun wanada aka samu sun yi auren jinsi guda za su fuskanci hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, yayin da su ma masu mu’amala ta jinsi daya za su fuskanci daurin da ya kai shekaru 10 a gidan yari.Akasarin ‘yan Nigeria suna adawa da mu’amala irin ta jinsi daya, don haka suke goyon bayan dokar da shugaban kasar ya sanya wa hannu. 

Ministar harkokin wajen kungiyar Taraiyyar Turai, Catherine Ashton
Ministar harkokin wajen kungiyar Taraiyyar Turai, Catherine Ashton REUTERS/Hamad I Mohammed
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.