Isa ga babban shafi
Tunisia

Firaministan Tunisiya ya yi murabus daga mukamin shi

Firaiyi ministan kasar Tunisia Ali Larayedh ya yi murabus daga kan mukaminsa a jiya laraba, a wani mataki da ake kallo a matsayin hanyar da za ta taimaka domin shawo kan rikicin siyasa da kasar ke fama da shi.Fiministan, wanda ke bayyanawa al’ummar kasar dalilansa na sauka daga kan mukaminsa, ya ce ko shakka babu gwamnatinsa ta yi aiki tukuru domin ciyar da kasar gaba kafin ya kai ga marabus din.Wannan ne karon da wani babban jami’I daga zababbiyar gwamnatin demokradiya ke yin murabus a kasar ta Tunisia, inda aka faro juyin juya halin kasashen Larabawa.A jawabinsa da aka watsa ta gidan talabijin na kasar Ali Larayedh ya ce ya tafiyar da alahakin da ‘yan kasar suka dora masa, a cikin wani yanayi da ya yi ta fuskantar matsi, to amma duk da haka, a cewar shugaban gwamnatin shi ta yi aiki domin ci gaban kasar ta Tunisia.Yin murabus din dai na daga cikin wata yarjejeniyar mayar da kasar kan kyakyawar turbar demokradiya bayan koma bayan rigingimu na siyasa da kasar ta yi fama da su sakamakon kashe Mohd Brahmi wani jigon ‘yan adawar kasar a shekarar da ta gabata. Yarjejeniyar dai ta tanadi cewa firaministan zai yi marabus ne bayan kwanaki 15 da sanya mata hannu.A tsawon watannin da suka gabata Jam’iyar Ennahda ta Firaiyi minista Ali Larayedh, ta fuskanci kalubale daga abokan hamayyar ta na siyasa, wadanda ke fatar ganin ta mika ragamar mulki sanadiyar yadda tattalin arziki kasar ke ci gaba da tabarbarewa. 

Tsohon Friministan Tunisia Ali Larayedh
Tsohon Friministan Tunisia Ali Larayedh REUTERS/Zoubeir Souissi/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.