Isa ga babban shafi
Tunisia

Ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin ‘Yan uwa Musulmi a Tunisia

Dubban ‘Yan adawa ne suka kaddamar da zanga-zanga a kasar Tunisia suna masu neman sai gwamnatin Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta Ennahda ta yi murabus, wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da ake kokarin gudanar da taron kasa domin kawo karshen rikicin kasar.

'Yan adawa suna zanga-zangar kin jinin gwamnatin 'Yan uwa Musulmi a Tunisia
'Yan adawa suna zanga-zangar kin jinin gwamnatin 'Yan uwa Musulmi a Tunisia REUTERS/Anis Mili
Talla

‘Yan adawar sun hada gangami ne a tsakiyar birnin Tunis cikin tsautsararan matakan tsaro, suna masu yada fatawar adawa da gwamnati.

Zanga-zangar ‘Yan adawa a yau Laraba ta rinjayi zanga-zangar masu nuna goyon bayan gwamnati da suka shirya gudanarwa domin karo da 'Yan adawa.

Zanga-zangar dai na zuwa ne kafin a bude taron kasa don magance rikicin siyasar kasar inda kasar ta shiga rudani bayan kisan wani dan Majalisar bangaren ‘Yan adawa Mohamed Brahmi.

A lokacin gudanar da taron kasar ana sa ran Firaminista Ali Larayedh ya yi murabus, don kawo karshen tankiyar da ake samu.

Fadar Firaministan ta sanar da cewar zai yi jawabi bayan taron, don warware rikicin siyasar kasar.

Game da makomar kasar da masu shiga tsakani suka shata, ana sa ran taron kasa da za’a gudanar zai kai ga samar da sabuwar gwamnatin kwararru ta rikon kwarya nan da tsawon mako uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.