Isa ga babban shafi
Tunisia

An gudanar da zanga-zangar karo da juna a Tunisia

A kasar Tunisia akwai zanga- zanga ta karo da juna da dubban ‘yan kasar suka gudanar inda magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta Ennahda mai mulki suka fito domin kare gwamnatinsu, yayin da kuma masu adawa suka hada gangami domin neman sauyin gwamnati.

dubban masu Zanga-zanga a kasar Tunisia
dubban masu Zanga-zanga a kasar Tunisia REUTERS/Anis Mili
Talla

Daruruwan magoya bayan Jam’iyyar Ennahda ne suka hada gangamin nuna goyon baya a birnin Tunis. Kamar yadda dubban masu adawa suka fito suna masu kira a rusa gwamnati.

Tunisia ta shiga damuwa ne tun lokacin da aka kashe madugun adawa Chokri Belaid, kuma wutar rikicin ta sake kunno kai ne bayan kisan Dan majalisa Mohamed Brahmi, da aka harba a ka a harabar gidansa.

A ranar Talata mai zuwa ‘Yan adawa sun yi kiran gudanar da gagarumar zanga-zanga domin neman kawo karshen gwamnatin Musulunci ta Jam’iyyar Ennahda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.