Isa ga babban shafi
Tunisia

An samu kudi Dala Miliyan 29 a asusun ajiyar matar Ben Ali na Tunisia

Gwamnatin Tunisia ta karbe kudi kimanin Dala miliyan 28.8 daga asusun ajiyar uwargidan hambararren shugaban kasar Tunisia Zine El Abidine Ben Ali. Kamfanin Dillacin labaran kasar na TAP yace an hannunta kudaden ga shugaba Moncef Marzouki.

Tsohon shugaban Tunisia Zine El Abidine Ben Ali
Tsohon shugaban Tunisia Zine El Abidine Ben Ali Reuters
Talla

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ali bin Fetais al-Marri, wanda aka nada domin jagorantar bankado kudaden da shugabannin da zanga-zanga ta yi awon gaba da su a kasashen Larabawa shi ne ya hannunta kudaden ga shugaba Moncef Marzouki.

Kamfanin Dillacin labaran TAP yace an gano kudaden ne a asusun bankin Laila Trabelsi, uwargidan Ben Ali a kasar Lebenon, wacce ta fice da iyalan shugaban zuwa kasar Saudiya a ranar 14 ga watan Janairun 2011 bayan kawo karshen mulkin shi.

Gwamnatin Tunisia tace kudaden al’umma ne aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.