Isa ga babban shafi
Tunisia

An cafke wasu mutane uku da ake zargin sun kashe Belaid

Mahukuntan kasar Tunisia sun ce sun cafke wasu mutane da ake zargin sun kashe Jagoran ‘Yan adawar kasar Chokri Belaid. Tun bayan kisan Belaid kasar Tunisia ta sake fadawa wani sabon rikicin Siyasa wanda ya kai har Firaminsitan kasar Hamadi Jebali ya yi murabus. Yanzu haka kuma Jam’iyyun siyasar kasar suna neman wanda zai gaje shi. 

Lokacin da 'yan sanda ke arangama da masu zanga zanga a Tunisia bayan kashe Chokri Belaid
Lokacin da 'yan sanda ke arangama da masu zanga zanga a Tunisia bayan kashe Chokri Belaid REUTERS/Anis Mili
Talla

Dangane da rikicin siyasar na Tunisia, Dr. Aminu Umar na babbar Kwaljin fasaha ta Kaduna ya yi tsokaci cewa za’a kwashe lokaci kafin a samu ci gaban Demokradiyya a kasashen Larabawa da suka kifar da gwamnatocinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.