Isa ga babban shafi
Tunisia

An dakatar da tashi da saukar jirgen sama a ciki da wajen kasar Tunisia

Harka sufuri jirga sama ta tsaya cik a dauka filayen jiragen sama a fadin kasar Tunisiya sakamakom yajin aiki na gama gari da al’umar tunisiya suka shiga, a dai-dai lokacin da za’a bine shugaban ‘yan adawa Chokri Belaid wadda aka kashe a makon jiya, al’amari da ya haddasa soke tashi da saukar jiragen sama a dauka fadin kasar.

taron mahalarta zana'izar  Chokri Belaïd madugun yan adawar Tunisiya da aka kashe.
taron mahalarta zana'izar Chokri Belaïd madugun yan adawar Tunisiya da aka kashe. REUTERS/Anis Mili
Talla

Wani jami’I a hukumar lura da sufurin jirgin sama a kasar ta Tunisiya ya tabbatawar kamfani dillanci labaru na AFP cewa yajin aikin ya kawo nakasu a duk harka sufurin na jirage da suke zirga-zirgar a ciki da wajen kasar, saboda ba ma’aikata da zasu duba irin wadannan jirage domi tashin su.

Dubban al’umar kasar ta Tunisiya sun fito tituna a fusace a yau don binne shugaban ‘yan adawa da aka hallaka al’amari dake neman kara dagula al’amuram siyasa bayan shekaru biyu da yin juyin juya hali a kasar ta tunusiya.

Don hana tarzoma An jibge motoci masu sulke na jami’an tsaro akan babban titi nan na Habib Bourguiba wadda shi ne wurin da akayi fito na fito a shekaru biyu da suka gabata al’amari da ya haddasa faduwa gwannati shugaba Zaid El Abidin a inda daga na guwar canji ta mamaye kasashen larabawa.

Wanna yaji aiki na gama gari da Babban Kungiyar kwadago a kasar Tuniya ta kira a na gani zai zama wani babban al’amari da zai kawo koma baya ga gwamnati prime ,inister Hamadi Jebali na jam’iyar ENNAHADA da ya nemi samar da sabbin jami’am gwannatinsa al’amari da wasu sassa na jami’iyarsa suka yi brus da shi.

Ita dai Jammiyar ENNAHADA ta yi fatali da zargi da iyalan Marigayi BELAID suka na cewa akwai hannu kososhin jammi’yar wajen hallaka shugaban na ‘yan adawa,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.