Isa ga babban shafi
Tunisia

Firaministan Tunisia ya yi murabus

Firaministan Tunisia Hamadi Jebali, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, bayan Jam’iyyarsa ta Ennahda ta ki amincewa da kudirin kafa gwamnatin kwararu kamar yadda ya yi alkawari. Saukar Jebali daga mukamin Firaminista ya sake jefa siyasar kasar cikin rudani, tun bayan kisan da aka yi wa shugaban ‘Yan adawa, Chokri Belaid a ranar Shida ga watan Fabrairu.

Hamadi Jebali Firaministan Tunisia
Hamadi Jebali Firaministan Tunisia AFP PHOTO / FETHI BELAID
Talla

“Na yi Alkawalin yin murabus, saboda rashin samun nasara ga kudiri na” inji Jebali.

A watan Janairun 2011 ne al’ummar Tunisia suka kifar da gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali bayan kwashe kwanaki suna zanga-zanga, kuma tun lokacin ne kasar ta shiga rudanin Siyasa da matsalar tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.