Isa ga babban shafi
Syria

Taron kasashe aminan Syria ya jadadda goyo bayansa ga 'yan tawaye

Kasashen da ke kiran kansu aminan Syria karkashin jagorancin Amurka, sun kammala taron da suka gudanar a birnin Istambul na kasar Turkiyya, inda suka jaddada cikakken goyon bayansu ga kawancen kungiyoyin ‘yan tawayen da ke yakar gwamnatin Basharul Assad.

Tarkacen gine-ginen a kasar Syria
Tarkacen gine-ginen a kasar Syria Reuters/Seddiq al-Shami
Talla

A lokacin wannan taro na birnin Istanbul, masu adawa da gwamantin Assad da suka hada da ‘yan tawaye da kuma fararen hula, su sake yin kira ga kasashen duniya da su goyi bayan shirin aikewa da sojojin kasa da kasa domin murkushe shugaba Assad a daidai wannan lokaci da alkalumma ke cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 70.
Yanzu haka dai kasashen Yamma cikinsu kuwa har da Amurka, na ci gaba da nuna shakku dangane da bai wa ‘yan tawayen na Syriya makamai saboda yiyuwar fadawar makamai a hannun kungiyoyin masu alaka da Alqa’ida musamman ma kungiyar nan mai suna Al-Nosra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.