Isa ga babban shafi
Tunisia

Kome ya tsaya Cik! A kasar Tunisia sakamakon gagarumin yajin aiki da akeyi.

Babbar kungiyar ma’aikatan kwadago a kasar Tunisia ta bukaci magoya bayanta da su gudanar da yajin aiki a yau juma’a domin nuna bacin ransu dangane da kisan da aka yi wa wani dan adawa sannan kuma dan Majalisar dokokin kasar ta hanyar harbe shi da bindiga a jiya.

Masu zaman dirshan a kan Tituna
Masu zaman dirshan a kan Tituna rfi/siv channa
Talla

Tuni dai wasu kamfanonin jiragen sama a kasar suka sanar da soke tashin jiragensu a yau sakamakon wannan kira da Kungiyar ta UGTT ta yi.

A jiya dai ne wasu mutane dauke da makamai suka harbe dan adawar mai suna Mohamed Brahmi, lamarin da ya haddasa mayar da martani daga sassa daban daban na duniya.

Wayewar Safiyar yau Jumu’a an bayyana yanda Manyan Titunan biranen kasar suka zama tsit! Jirage kuma basa tashi a filayen Jiragen kasar sakamaon wannan yajin aikin da Uwar kungiyar kwadago ta kira a kasar, domin nuna rashin goyon baya ga kisan da aka yiwa wani jigon ‘yan adawa Mohammad Brahimi.

An dai Bindige Brahmi dan shekaru 58 ne a wajen Gidan sad a ke a Ariana kusa da Tunis ta hanyar amfani da Babur.

Rahotannin dake fitowa daga kasar ta Tunisia na nuna cewar duk da kananan Shagunan da aka buda domin amfanin Musulmi masu Azumin Ramadana sun kasance a rufe, kananan Kasuwanni kuwa kowacen su a garkame.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.