Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Dakarun Faransa sun isa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Hukumomi dakarun kasar Faransa su 800 sun isa kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a kasar inda ake kai hare hare ga mutane da yiwa mata fyade a yankuna daban daban. 

Wani sojin Faransa yana sintiri a birnin Bangui dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Wani sojin Faransa yana sintiri a birnin Bangui dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya REUTERS/Joe Penney
Talla

Da ma akwai dakarun Faransan su 400 a jibge a kasar lamarin da ya ake dasa alamar tambayar yadda suka kasa dakile hare ahren.

Shugaban kasar Michel Djotodia ya bukacin al’umar kasar da su bada hadin kai ga hukumomin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin akalla mutane 400,00 suka fice da gidajensu domin gujewa rikicin.

A watan Maris din da ya gabata ne ya Djotodia ya jagoranci hambarar da gwamnatin Francois Bozize inda ya nada kansa a matsayin shugaban rikon kwarya ya kuma soke kungiyar ‘yan tawayen kasar.

Sai dai Djotodia ya gaza wajen kakkabe abokanansa da suka yi juyin mulki wandanda suka ci gaba da kai hare hare a wasu sassan kasar, lamarin da ya haifar da kungiyoyin mayakan sa ka domin su kare kansu.

Djotodia shine shugaba Musulmi na farko da yake mulkar kasar wacce fiye da kashi 80 daga cikin mutanen kasar mabiya addinin kirista ne.

Kasashen da kungiyoyin duniya na fargabar barkewar rikicin addini a kasar saboda mafi aksarin ‘yan tawayen da suka rage Musulmai ne yayin da mayakan sa kai da ke kare kansu kiristoci ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.