Isa ga babban shafi
Sierra Leon

An gurfanar da ministan ilimi a Sierra leon saboda zargin fyade

Wata kotu a kasar Sierra Leone ta gurfanar da mataimakin Ministan ilimin kasar, kan zargin aikata laifin fyade a kan wata dalibar jami’a kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.bayan tube shi daga mukamin nashi, kotu a kasar ta hana bada belin mataimakain ministan Mamoud Tarawali, yanzu haka dai yana tsare a gidan yari duk da cewar ya musanta aikata wannan laifin da ake tuhumarsa da shi.‘Yan sanda sun ce dalibar da ta shigar da wannan karar dai, tana da shekaru 24 a Duniya, inda ta shaida wa hukumomi cewar lamarin ya faru ne a wani gida. A halin yanzu kasar ta Sierra Leone tana kan farfadowa daga yakin basasar tsawon shekarun da ta yi fama da shi, inda aka aikata munanan laifufuka cin zarafin bil’adama a cikinsa, da suka hada da fyade ga mata manya da yara  

Shugaban kasar Saliyo, Ernest Koroma
Shugaban kasar Saliyo, Ernest Koroma REUTERS/Joe Penney
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.