An cire dokar hana amfani da wayar sadarwa a jihar Adamawan Najeriya
Hukumomin soja a Tarayyar Najeriya, a jiya alhamis sun amince da bai wa jama’ar jihar Adawa wato daya daga cikin jihohi uku da aka kafawa dokar ta baci, damar yin amfani da wayar sadarwa, bayan share kusan watanni uku a cikin wannan hali.
Wallafawa ranar:
To sai dai har yanzu sauran jihohi biyu da wannan doka ta shafa wato Yobe da Borno, kamar yadda kakakin rundunar tsaron Najeriya Burgediya Janar Chris Olukolade ya shaida wa sashen Hausa na RFI, za su ci gaba da kasancewa a karkashin dokar da ke haramta yin amfani da hanyioyin na sadarwa.
Daukar matakin sassauta dokar a jihar Adamawa ya biyo bayan ci gaban da aka sama ne da kyautatuwar tsaro a jihar a cewar Janar Olukolade.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu