Isa ga babban shafi
Najeriya

An kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Boko Haram da gwamnatin Najeriya

Hukumomin Najeriya sun sanar da cewa sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad, da ake kira Boko Haram. Ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki ya ce gwamnatin cim ma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da bangarorin biyu suka yi.  

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a zauren taron tattalin arzikin Duniya a birnin Davos
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a zauren taron tattalin arzikin Duniya a birnin Davos REUTERS/Pascal Lauener
Talla

Ya kuma kara da cewa kungiyar ta amince ta ajiye makamanta domin tabbatar da cewa an cim ma wannan yarjejeniyar.

“Mun zauna mun tattauna sun kuma aminta, su mutanen Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad, da ake kira sun yarda cewa za a ajiye makamai, za a daina wannan fafatawa da ake yi.”

Ya kara da cewa gwamnati anata bangaren ta amince da wannan matsaya da kungiyar ta dauka inda ta yi alkawarin sassauta ayyukan dakarunta.

“Gwmnati ta yi na’am da wannan kuma za ta dauki matakan da itama za ta sa dakarunta su sassauta abubuwan da su ke yi izuwa lokacin izuwa lokacin da za a zo a ajiye makamai.

A bangaren kungiyar ta Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad, Imam Muhammadu Marwana ya ce lallai an kulla wannan yarjejeniya.

“Wannan tsagai wuta in sha’allahu daga lokacin da nake magana da kai (wakilin Radiyo Faransa) an tsagaita wuta sakamakon tattaunawa da aka yi domin samun salama a cikin wannan tafiya.”

Imam Marwana ya kara da neman a yafe musu irin rashen rashen rayuka da suka faru a kasar.

“Al’uma kuma duk wanda ya rasa rayuwarsa da dan’uwansa ko da sauransu muna neman da a yafe mana mu namu wanda aka yi mana mun yafe a matsayi na na Muhammad Marwana.”

Wannan yarjejeniyar tsagaita wuta na zuwa ne bayan kashe wasu dalibai da Malaminsu da aka yi a Jihar Yobe, wanda kungiytar ta nisanta kanta da wannan lamari.

“Abinda ya faru a wannan makaranta, bamu da hanua ciki, na fada da babbar murya bamu da hanu a ciki.” Inji Marwana.

A game da harin da aka kai a makarnatar a yanzu gwamnatin Jihar Yobe, ta bada umurnin rufe daukacin makarantun Sakandaren Jihar, sakamakon harin da aka kai a Mamudo, wanda ya hallaka dalibai 22 da malami guda.

Gwamnan Jihar, Ibrahim Geidam ya bayyana haka, yayin da ya ziyarci makarantar.

Matakin na gwamnatin Jihar Yobe, ya biyo bayan wani hari da wasu ‘Yan bindiga suka kai Makarantar.

A lokacin kai ziyarar, Geidam da ya ziyarci ya ce ba za’a bude makarantun ba sai a watan Satumba, bayan sun kammala shirya yadda za’a samar da tsaro wa dalibai da kuma malamansu.

Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da harin, ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin soji da su bada umurnin mayar da layin sadarwa a Jihar, wanda ya ce zai taimakawa jama’a wajen tseguntawa jami’an tsaro abinda ke faruwa.

Gwamnan ya kuma bukaci jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen kare lafiyar al’umma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.