Faransa za ta karfafa dangantaka da kasashen Afrika a taron Congo
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai nemi karfafa dangantakar kasuwanci da Diflomasiya da kasashen Afrika masu Magana da harshen Faransanci a wani taro da kasashen tare da Faransa za su gudanar a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Wallafawa ranar:
Kimanin Kasashen Afrika masu Magana da harshen Faransanci 70 ne ake sa ran za su kai ziyara birnin Kinshasha domin halartar taron na kwanaki biyu inda kasashen za su yi kokarin fito da hanyoyin magance rikicin ‘Yan tawayen Congo da Mali.
Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi alkawalin taimakawa ga ci gaban Demokradiyya a Afrika da ke fama da magudin zabe.
Kasar Faransa dai tana cikin manyan kasashe da ke zuba hannayen jari a kasashen Afrika. kuma duk da matsalar tattalin arziki da ya shafi kasar amma Faransa tana taka rawa wajen taimakawa da dakarun Soji musamman a kasashen Senegal da Chad da Cote d'Ivoire da Djibouti.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu