Amurka ta yi gargadin Boko Haram suna shirin kai hare hare a Abuja
Ofishin Jekadancin Amurka a Najeriya ya yi gargadin kungiyar Boko Haram Suna shirin kai hare hare a birnin Abuja a wuraren shakatawar Turawa a wani sako da Ofishin ya yada a Intanet.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
“Ofishin jekadancin Amurka ya samu sakon kungiyar Boko Haram sun shirin kai hare hare a Abuja, Najeriya a wuraren da Turawa ke sauka,” Sakon gargadi da Amurka ta yi ga Amurkawa.
A watan Nuwamba Amurka ta aiko da irin wannan gargadin wanda ya janyo suka amma babu wani hari da aka samu a birnin Abuja a lokacin.
A Najeriya an dade ana zargin Kungiyar Boko Haram da kai hare hare a arewacin kasar inda kungiyar kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International tace kungiyar Boko Haram ta kashe mutane sama da 1,000 tun fara kaddamar da hare hare a shekarar 2009.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu