Isa ga babban shafi
Gabon

An kafa sabuwar gwamnatin kasar Gabon

Sabon Fira Ministan Gabon, ya yi gagarumar garambawul ga Gwamnatin kasar, inda ya sauke wasu manyan ministocin kasar, cikinsu harda sirikin Tsohon shugaban kasa, Omar Bongo, wato Paul Toungui.Shidai Toungui tun shekarar 1990 yake rike da mukamin Minista a kasar. 

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba AFP / Hakon Mosvold Larsen
Talla

Sakataren harkokin mulki na fadar shugaban kasa Laure-Olga Gondjout ya ce gwamnatin kasar yanzu ta kunshi ministoci 29, da suka hada da Fira Ministan kasar Raymond Ndong Sima, wanda shugaba Ali Bongo ya nada ranar Litini.

Sabon Fima Minista Ndong Sima dan shekaru 56 da haihuwa, kafin nadin shi ne ministan harokokin noma, kuma yanzu ya maye gurbin tsohon Fira Minista Paul Biyoghe Mba.

Mahaifin shugaban kasar na yanzu Marigayi Omar Bango ya fiye da shekaru 40 yana mulkin kasar ta Gabon mai arzikin man fetur tun daga shekarar 1967 zuwa mutuwarsa cikin shekara ta 2009, a kasar wadda Faransa ta yi mata mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.