Isa ga babban shafi
Najeriya

An ji karar fashewa da musayar Albarussai a Kano

Rahotanni Daga birnin Kano, da ke Najeriya sun ce an samu fashewar bama bamai da  harbe harbe a unguwar Badawa, makwanni bayan harin da ya lakume rayukan mutane kusan 200. Kamfanin Dillancin labaran Faransa, ya ruwaito cewar an samu fashewar bama bamai shida, da kuma jin amon harbin bindiga kafin Sallar Asubar yau Laraba, a unguwar Badawa.

Wani harin da Kungiyar Boko Haram ta kai a Birnin Kano wanda ya lakume rayukan mutane 185
Wani harin da Kungiyar Boko Haram ta kai a Birnin Kano wanda ya lakume rayukan mutane 185 Reuters/Stringer
Talla

Sai dai har yanzu babu labarin abun da ya Haifar da fashewar, sai dai wasu mazauna birnin Kano sun ce Jami’an tsaro ne suka kai samame a wani wuri da suke tunanin mafakar ‘Yan kungiyar Boko Haram ne a unguwar Tinshama kusa da Badawa inda mafi yawan mazauna unguwar Musulmi ne da Kirista.

Bala Haruna Wani mazauni unguwar Badawa yace an girke ‘Yan sanda da Sojoji da ke sintiri a unguwar.

A kwanan baya an kai wani hari a Birnin Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 185 da Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin daukar alkakin kai wa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.