Isa ga babban shafi
Senegal

Al’ummar Senegal na ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da Wade

Masu Zanga-zangar adawa da Tazarcen Abdoulaye Wade a kasar Senegal na ci gaba da arangama da ‘Yan Sandan kasar, inda ‘Yan Sandan ke amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin tarwatsa masu zanga-zanga bayan kammala salla a wani masallaci a birnin Dakar.

Masu adawa da Tazarcen Wade a Senegal a harabar masallacin da 'Yan Sanda suka harba hayaki mai sa hawaye
Masu adawa da Tazarcen Wade a Senegal a harabar masallacin da 'Yan Sanda suka harba hayaki mai sa hawaye AFP/ Seyllou
Talla

Kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP, ya ruwaito cewa, an dauki wani wanda ya suma sakamakon harbi.

Wannan wata sabuwar kazamar zanga-zanga ce da aka kaddamar inda ‘yan kasar ke neman haramtawa shugaba Abdoulaye Wade mai shekaru 85 na haihuwa tsayawa takarar shugaban kasa karo na uku.

Sabon rikicin ya barke ne a wajen wani Masallci a Dakar inda masu zanga-zangar suka ce ‘Yan sanda sun harba masu hayaki mai sa hawaye.

Daga bisani ne Ministan cikin gida Ousmane Ngom ya nemi gafarar abinda ‘Yan sandan kasar suka aikata tare da neman ‘Yan siyasar kasar kauracewa gudanar da yakin neman zabe a masallatai.

Bayan kammala wa’adin shugabancinsa na biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya shata, Shugaba Wade yace gyaran fuskar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 2008 ya nuna yana iya sake neman wasu wa’adi biyu bayan kwashe shekaru yana shugabancin kasar.

A ranar 27 ga watan Janairu ne kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa shugaban zai iya sake neman wa’adi na uku akan karagar shugabancin kasar.

Kungiyar Tarayyar Afrika tace zata tura tawagar sa ido karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Cip Olusegun Obasanjo zuwa Senegal a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu. Tuni wasu daga cikin tawagar masu sa idon suka isa kasar amma a ranar Talata ne Obasanjo zai kai ziyara Dakar babban birnin kasar, kamar yadda kungiyar AU ta sanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.