Isa ga babban shafi
Senegal

Wade ya yi watsi da bukatar janye takarar shi a Senegal

Shugaban Kasar Senegal Abdoulaye Wade, ya yi watsi da kiran da ake masa na janye takarar shugaban kasa, inda yace kasashen Faransa da Amurka, basu da hurumin sa shi ya janye.

Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade a yakin neman zaben shi a Dakar
Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade a yakin neman zaben shi a Dakar REUTERS/Joe Penney
Talla

Yayin da yake kaddamar da yakin neman zaben sa, Wade yace baya bukatar goyana baya kasahsen Yammacin duniya, sai na ‘Yan kasar Senegal.

Shugaban yana ci gaba da fuskantar suka daga ‘yan adawa.

Luis Thomas Cisse, na Jam’iyar adawa ta Socialists, ya danganta tazarcen shugaban matsayin juyin mulki.

A cewar mista Thomas wannan juyin mulki ne ga kundin tsarin mulki, bayan kotun koli ta ba shugaban damar tsayawa takara.

A baya dai kasashen Faransa da Amurka suna goyon bayan shugaban ne amma yanzu sun bayyana damuwarsu tare da neman shugaban kasar Senegal ya dawo hannun matasa.

Yanzu haka ‘Yan takara 14 ne aka tantance zasu tsaya takara a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu da suka hada da fitatten mawakin kasar Youssou Ndour wanda aka yi watsi da takarar shi amma har yanzu yana ci gaba da jagorantar gangami domin adawa da tazarcen Wade.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.