Isa ga babban shafi
Senegal

Yan Sanda sun Fafata da Masu Zanga Zanga

Jiya Asabar aka shafe kwanaki hudu ana kai ruwa rana tsakanin ‘yan sandan kasar Senegal da masu zanga zangar dake nuna adawa da sake takarar Shugaba Abdoulaye Wade, a karo na uku.

REUTERS/Joe Penney
Talla

An haramta wa masu zanga zangar hallara a dandalin Dakar babban birnin kasar, kuma tashin hankalin ya yi sanadiyar hallaka wani matashi, a garin Kaolack birnin na biyu mafi girma a kasar.

Jami'an kula da kiwon lafiya sun ce mutane masu yawa sun jikata, yayin da Shugaba Wade dan shekaru 85, ya tsaya kai da fata sai ya sake neman wa’adi na uku na karin wasu shekaru biyar, yayin zaben ranar Lahadi mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.