Isa ga babban shafi
ECOWAS

Shugabannin ECOWAS zasu gudanar da Taronsu a Abuja

Shugabanin kasashen Afrika ta Yamma, na kungiyar ECOWAS, zasu gudanar da taronsu a Abuja, inda ake saran zasu zabi sabon shugaba, saboda kawo karshen wa’adin Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wani batu da ake tunanin zai mamaye zauren taron shi ne matsalar tsaro a Yankin Sahel da matsalar ‘Yan fashin Jiragen Ruwa, da kuma tabarbarewar al’amurran siyasa a kasar Senegal wanda ke fuskantar zabe.

Za’a dai kwashe kwanaki biyu ne ana gudanar da taron amma kuma a ranar Juma’a ne shugabannin zasu zabi sabon Shugaban Kungiyar ta ECOWAS.

Ana kuma sa ran shugabannin zasu zabi wanda zai gaji shugaban gudanarwar kungiyar James Victor Gbeho na Ghana.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne kuma Ministocin harakokin wajen kasashen zasu gudanar da taro bayan kammala taron shugabannin kasashen na ECOWAS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.