Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar-Benin

Matsalar tsaro a Najeriya yasa Direbobin Benin shiga wani hali a Nijar

Yanzu Haka direbobin motocin Janhuriyar Benin, na fuskantar mawuyacin hali a Jamhuriyar Nijar, sakamakon matsalar tsaron da ake samu a Najeriya, wasu Direbobi da dama da ke dauke da kaya sun ce sun kwashe sama da wata guda ba tare da an sauke kayan ba.

MD Abubakar Sabon Sufeto 'Yan sandan Najeriya
MD Abubakar Sabon Sufeto 'Yan sandan Najeriya RFI Hausa
Talla

04:02

Rehoton Rakiya Ibrahim

Matsalar tsaro da rikicin boko Haram a Najeriya ya shafi yawancin kasashe da ke makwabtaka da kasar musamman Nijar da Jamhuriyyar Benin da Kamaru.

A cewar Rakiya Ibrahim Wakiliyar Rediyo Faransa a Maradi, tace akwai Direbobin manyan motoci da suka kwashe tsawon wata biyu saboda haramta masu sauke kayan da suka dauko daga Kwatano na ‘Yan kasuwar Nijar da Najeriya.

Direbobin dai sun koka da irin halin da suka shiga na rashin abinci da ruwan sha saboda wannan matsalar.

Mahukuntan Nijar da Najeriya a kan iyakar Maradi dai sun dauki wannan matakin ne saboda hasashen da ake yi game da wanzuwar kungiyar Boko Haram a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.