Jonathan ya gana da Manyan Jami’an tsaro
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wata ganawar gaggawa da Jami’an tsaron kasar domin tattauna matsalar tsaro a kasar musamman game da hare haren da aka kai a ranar Kirsemeti. Shugaban yana kokarin lalubo hanyar magance zubar da jinin ‘Yan Najeriya, inda ake saran kara kaimi don magance matsalar tsaro da ke barazana ga al’ummar kasar.
Wallafawa ranar:
Abubakar Tsav, Tsohon kwamishinan 'Yan Sandan Lagos
A lokacin da yake ganawa da Manema Labarai, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Hafiz Ringim, yace shugaba Jonathan ya damu matuka game da kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, akan haka ne ya gayyace su domin tattauna yadda zasu shawo kan matsalar.
Ana kalubalantar gwamnatin Jonathan wajen rashin shawo kan matsalar Kungiyar Boko Harama. Da ake zargin kaddamar da hare hare a Arewacin Najeriya da birnin Abuja babban birnin kasar.
Barr. Solomon Dalung
A ranar Talata wasu wadanda ba’a tantance ba sun kai wani hari a makarantar Islama a kudancin kasar Jahar Delta, wanda y yi sanadiyar raunata yara kanana guda bakwai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu