Isa ga babban shafi
Najariya

Kotu ta yi watsi da karar CPC game da kalubalantar zaben Jonathan

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da daukaka karar da Jam’iyyar CPC ta shigar domin kalubalantar sakamakon zaben Shugaba Goodluck Jonathan da aka gudanar a watan Afrilu, bayan zargin samun kara-kurai da neman sake zaben.

Dan Takaran Shugabancin Nigeria na CPC Janar Muhammadu Buhari
Dan Takaran Shugabancin Nigeria na CPC Janar Muhammadu Buhari RFI/Hausa/Bashir
Talla

A cewar Mai sha’ria Olufunmilayo Adekeye, babu wasu kwararan hujjoji da CPC ta gabatar don haka suka yi watsi da karar.

00:34

Janar Muhammadu Buhari

Jam’iyyar adawa ta CPC ta yi zargin magudi da samun kura-kurai a zaben da aka gudanar a watan Afrilu inda Jam’iyyar ta bukaci soke zaben. Dan takarar Jam’iyyar ne Muhammadu Buhari ya zo na biyu.

Janar Buhari wanda tsohon shugaban kasa ne a zamanin mulkin soja tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985 yace hukuncin Kotun yana da Nasaba da siyasa.

00:52

Ministan yada labarai Labara Maku

Bashir Ibrahim Idris

Gwamnatin Najeriya ta bayyana bacin ranta ga kalaman Janar Muhamadu Buhari, kan hukuncin kotun kolin kasar, dangane watsi da Shari’arsu tare da hallata Jonathan matsayin wanda ya lashe zaben shugaban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.