Isa ga babban shafi
Nigeria

Mutane 68 sun hallaka cikin rikicin Najeriya kuma bam ya fashe ranar Kirsemeti

Ana kyautata zaton mutane masu yawa sun hallaka yayin da bam ya tarwatse a wajen ibadar mabiya addinin Krista yayin bikin Kristimeti na yaua a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.Zuwa yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka hallaka ko kuma suka jikata ba.

© Reuters/Afolabi Sodtunde
Talla

Bayanai daga Tarayyar ta Najeriya na tabbatar da cewa dauki ba dadi tashin hankalin da aka samu cikin makon da ya gabata ya yi sanadiyar hallaka mutanen kusan 68 cikin yankin Arewa maso gabashin kasar.

Hukumomin da majiyoyin asibiti da masu raji kare hakkin bil Adama ke bada alkaluman. Tahsin hankalin ya faro ranar Alhamis a garin Damaturu fadar gwamnatin Jihar Yobe ya bazu zuwa garin Potiskum da Maiguduri fadar gwamnatin Jihar Borno.

Babban habjon sojan Nigeria Lt Gen Azubuike Ihejirika ya bayyana cewa mutane 58 suka hallaka cikin kwanaki biyu na tashin hankalin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.