Isa ga babban shafi
Najariya

Kiristocin Najeriya sun ce zasu kare kansu daga hare hare

Kungiyar kiristocin Najeriya, ta zargi Gwamnatin kasar da gazawa wajen kare ‘yayanta daga hare haren da ake kai musu a sassan kasar. Bayan ganawa da shugaba Goodluck Jonathan shugaban kungiyar yace sun umurci mabiyansu da su kare kansu daga irin wadannan hare hare, inda ya zargi shugabanin Musulmin Arewacin Najeriya da rashin daukar mataki.

Harin Kirsemeti da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai wa a Cocin Mandella Suleja kusa da Abuja
Harin Kirsemeti da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai wa a Cocin Mandella Suleja kusa da Abuja Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

00:46

Shugaban Kungiyar Kirista Pastor Oritsejafor

A cewar Pastor Ayo Oritsajafor babu wani abinda ya rage wa Kiristocin Najeriya illa mayar da martani idan har aka ci gaba da kai masu hare hare.

‘Yan sandan Najeriya sun ce an kai wani hari a wata makarantar koyar da Arabiya a Jahar Delta kudancin kasar, harin da ya raunata yara kanana guda shida.

Wannan kuma na zuwa ne bayan kai harin Bom a ranar Kirsemeti da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40 a Suleja kusa da Abuja babban birnin kasar.

02:32

Rehoton Wakilinmu Kabir Yusuf Daga Abuja

A lokacin da yake mayar da martani Shugaba Goodluck Jonathan yace gwamnatinsa tana iya kokarinta tare da taimakon kasashen Afrika da suka yi fama da hare hare domin taimakawa Najeriya shawo kan matsalar.

Matakin da kungiyar Kiristoci ta dauka kan iya haifar da rikicin kabilanci a cikin kasar da kan iya raba ta gida biyu tsakanin Musulmi da kirista.

Shugabannin Kiristocin sun yi kira ga gwamnatin kasar domin daukar mataki akan kungiyar Boko Haram da ake zargin kai hari a wajajen ibadarsu inda Pastor Oritsejafor ya danganta hare haren a matsayin kaddamar da yaki ga mabiya addinin Kirista.

A ranar Talata ne Sarkin Musulmi Alh. Abubakar Sa’ad 111 ya gana da shugaba Jonathan bayan kai harin Kirsemeti, amma shugaban yace babu wani sabani ko rikici sakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi.

A cewarsa wannan rikici ne tsakanin shedanu da mutanen kwarai tare da kiran hadin kan juna domin yaki da masu neman tayar da hankali a cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.