Isa ga babban shafi
Rwanda

Kotun Duniya zata saki tsohon dan Tawayen Rwanda

An jima kadan a yau Jumma'a, ake sa ran kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta saki jagoran ‘yan tawayen kasar Rwanda Callixte Mbarushimana.

Callixte Mbarushimana
Callixte Mbarushimana AFP PHOTO/ANP/Jerry Lampen
Talla

Lauyan Mbarushimana ya tattabatar da hakan, inda ya ce da misalin karfe 4:30 na yamma agogon TU ake sa ran zai sauka a filin jirgin sama na Roissy a kasar Faransa, wanda kuma shine na farko da kotun ta zarga aka kuma sake shi.

Tun kusan shekara guda ake tsare da Mbarushimana, mai shekaru 48, inda yake fuskantar zargi 13, da suka shafi laifukan yaki kan bil adam, amma a yau kotun ta yi watsi da dukkan zargin saboda rashin gamsassun shaidu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.