Isa ga babban shafi
Rwanda

Kagame ya yi na’am da kiran yin tazarce

Shugaban Kasar Rwanda, Paul Kagame, yace ba shi da wata matsala ko kadan, da masu kiran sauya kundin tsarin mulkin kasar, don bashi damar yin tazarce a karo na uku.

Paul Kagame, a ziyarsa kasar faransa
Paul Kagame, a ziyarsa kasar faransa REUTERS/Philippe Wojazer (
Talla

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Uganda, shugaba Kagame yace, kowa na da damar fadin albarkacin bakinsa, kuma shi bashi da hurumin hana ‘Yan kasar abinda suke so.

Rahotanni sun ruwaito Ministan tsaron cikin gida, Sheikh Fazil Musa Harerimana na bukatar ganin an sauya kundin don bai wa Kagame damar ci gaba da mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.