Isa ga babban shafi
Rwanda

Yan adawa sun fara mayar da martani game da sakamakon zaben shugaban kasa

Wata rikakkiyar yar adawar kasar Rwanda dake karkashin kulawar shara’a Victoire Ingabire ta yi kiran masu zuba jari a kasar, da su yi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar, na ranar Litanin da ta gabata, wanda shugaban kasar Paul Kagame yace ya lashe da kashi 93 cikin 100.Mme Ingabire wace taso ta tsaya takara a zaben da yan adawa suka kauracewa, ita ce shugabar jamiyar Forces Démocratiques Unifiées FDU, jama’iyar da mahukumtan kasar basu amincewa ba.A daren jiya Laraba a birnin Kigali babban birnin kasar a dai dai lokacin da magoya bayan shugaba Kagame ke murnar samun nasarar wani gurneti ya tarwatse inda mutane 7 suka jikkata.

Victoire Ingabire 'yar adawar kasar Rwanda
Victoire Ingabire 'yar adawar kasar Rwanda AFP/Bertrand Guay
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.