Isa ga babban shafi
Rwanda

Hukumar zabe ta tabbatar da Shugaba Kagame ya lashe wa’adi na biyu

Hukumar zaben kasar Rwanda ta tabbatar da cewa shugaba Paul Kagame ya lashe sabon wa’adi na biyu na wasu shekaru bakwai.Shugaban dan jam’iyyar (Rwanda Patriotic Front) RPF, ya samu kashi 93 cikin 100 na daukacin kuri’un da aka kada, yayin zaben ranar Litinin data gabata.Dan takatarar jam’iyyar Social Democratic Party, Jean Damascene Ntawukuriryayo, ya zo na biyu da kashi 5.15 cikin 100, yayin na Prosper Higiro na jam’iyyar Liberal Party ke matsyai na uku da kashi 1.37 cikin 100, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana a yau Laraba.Sakataren hukumar zaben kasar ta Rwanda, Charles Munyaneza, ya ce dan takara na hudu na samu adadin wanda bai kai kashi daya cikin 100 ba.Sakataren hukumar zaben ta NEC Mr Charles Munyaneza ya bayyana cewa, shugaba Kagame ya samu yawan kuru’u miliyan 4 da dubu 635.560 wada hakan ke nuna cewa ya samu kashi 93,08% na yawan kuru’un da aka kada, wanda hakan ya bashi damar sake gyara zama kan kujerar shugabancin kasar na wasu shekaru 7 nan gaba.Tun cikin daren ranar Litinin da a ka gudanar da zaben, magoya bayan shugaba Paul Kagame suka fara tsallen murnar nasara.Masu sako ido kan zabe daga kungiyar kasashen raina Birtaniya (Commonwealth) sun soki yadda ake zallaza wa 'yan adawa, amma sauran kungiyoyin sun taba da shirye shiryen zaben.A wani labarin, Shugaba Kagame ya tsame hanun gwamnatinsa daga kisan gillar da akayi wa wani dan jarida, Andre Kagwa Rwisereka cikin watan jiya.Kasar ta Rwanda dake yankin gabashin Afrika, tayi fama da kisan kare dangi cikin shekarar 1994 inda a ka hallaka kimanin mutane 800,000 cikin kwanaki 100, 'yan kabilan Tutsi da Hutawa masu sassaucin ra'ayi. Kungiyar RPF ta Paul Kagame ta jagoranci kawo karshen lamarin. 

Shugaban Rwanda Paul Kagamé tare da 'yan jaridu
Shugaban Rwanda Paul Kagamé tare da 'yan jaridu Photo : James Akena / Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.