Isa ga babban shafi
Rwanda

Shugaban Rwanda Kagame ya musanta hanu cikin kisan wani dan Jarida

Shugaban Kasar Rwanda Paul Kagame yau Litinin ya musanta zargin da ake yi wa Gwamnatinsa cewa tana da hanu wajen kashe wani Dan Jarida mai yawan sukan sa.

Shugaban Rwanda Paul Kagame
Shugaban Rwanda Paul Kagame REUTERS/Philippe Wojazer (
Talla

Dan Jaridan mai suna Charles Ingabire, dan shekaru 32 da haihuwa, kafin mutuwar shi ne Editan Jaridar Inyenyeri, wanda aka harbeshi da bindiga, ranar daya ga wannan watan Disamba.

Shugaba Kagame ya ce jami'an tsaro da suka gudanar da binciken musabbabin mutuwar dan jaridan sun gano cewa wai sata ce dan jaridar yayiwa wata Kungiya da yake wa aiki, ya gudu aka kama shi.

Shugaban kasar ta Rwanda Kagame ya bayyana wadannan kalamai yayin taro da 'yan jaridu a birnin Kampala na kasar Uganda, inda ya kai ziyara aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.