Isa ga babban shafi
Najeriya

Fushin ‘Yan Najeriya kan cire Tallafin Man Fetir

Abubuwa sun fara yin nisa ga tunanin yawancin ‘yan Najeriya da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa, inda gwamnatin kasar ke kokarin cim ma kudirinta na janye tallafin Mai hanya daya da ‘yan Najeriya ke ganin suna more arzikin Man fetir din da Allah ya azurta su da shi.Wasu masana tattalin arziki suna ganin cire tallafin man fetir wanda zai haifar da Karin farashin Mai a kasuwa ita ce hanyar da za’a bi wajen samar da ingantaccen sauyi a NajeriyaSai dai idan aka kwatanta halin da ‘yan Najeriya ke ciki, yawancin ‘yan kasar suna rayuwa ne kasa da Dala biyu a rana, wasu suna ganin cire tallafin da Karin farashin man Fetir babu abinda zai haifar sai Karin wahala da jefa su cikin kuncin rayuwa.Akwai biliyoyan kudade da Najeriya ke samu ta hanyar Man Fetir amma har yanzu gwamnatin kasar ta kasa shawo kan matsalar wutar lantarki, kullum kuma mutane sai mutuwa suke a saman hanyoyin sufurin kasar saboda rashin kyau.Idan kai mai nazari ne da wuya ka gano gaskiyar al’amarin domin danyen mai kalilan ne Najeriya ke tacewa a cikin kasar al’amarin da ake zargin cin hanci da rashawa ne tattare da gwamnati tare da rashin kula da matatun man kasar inda gwamnatin ke fita da danyen mai kuma take shigowa da Man fetir daga kasashen waje.Ana sa ran biliyoyan kudaden da ake samu daga tallafin man ya haifar da saukar farashin fetir duk da ana shigowa da man da farashinsa.Gwamnatin Najeriya tace ta kashe kudi Dala Biliyan takwas na tallafin Man Fetir a bana amma kuma babu wani ci gaba da ‘yan Najeriya suka gani a kasa.‘Yan kasar na zargin kudaden tallafin na zuwa ne aljihun wasu manyan Jami’an gwamnati.A badi za’a fara cire tallafin kamar yadda Ministan kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar ma’aikaciyar Bankin duniya ta ayyana.Matakin da wasu masana tattalin arziki suka yi na’am da shi inda suka bayyana cewa za’a samu damar amfani da kudaden domin samar da ayyukan ci gaba a kasar.Sai dai wasu suna ganin gwamnati ya dace ace ta fara janye kudaden da take biyan ‘yan Majalisu inda aka danganta cewa Senata yana karbar kudi Dala $140,000 a wata.Tuni dai kungiyoin kwadago a Najeriya suka la’anci matakin cire tallafin inda suke kalubalantar gwamnati yadda zata yi amfani da kudaden idan har ta cire tallafin. 

Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala
Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala REUTERS/Brendan McDermid
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.