Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta tabbatar da zaben Jonathan a Najeriya

Kotun daukaka kara a Niajeriya ta yi watsi da karar da Jam’iyyar CPC ta shigar na kalubalantar zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Aprliu bayan hukumar zaben a kasar ta bayyana sunan Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben.A ranar 8 ga watan Mayu ne Jam’iyyar adawa ta CPC ta shigar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben Jahohi 14 da sakamakon zaben ya nuna Jonathan ne ya lashe zaben, sai dai kuma kotun daukaka kara tace ingataccen zabe aka gudanar. 

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan,lokacin da zai kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa a kauyensa Otuoke,a Bayelsa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan,lokacin da zai kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa a kauyensa Otuoke,a Bayelsa. Reuters/Joseph Penney
Talla

00:41

Farfesa Rufa'i Alkali Sakataren PDP

Tun bayan bayyana sakamakon zaben ne aka samu barkewar rikici a arewacin kasar, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 500 tare da kona gidaje da wuraren ibada.

Alkalan kotun sun kafa hujja ne akan cewar jam`iyyar CPC ta kasa kafa hujjoji masu gamsarwa da za su tabbatar da zarginta an tabka magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

00:44

Buba Galadima Sakataren Jam'iyyar CPC

Sai dai kuma jam’iyyar CPC tace zata sake daukaka kara domin ci gaba da kalubalantar zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.