Isa ga babban shafi
Nigeria

An cafke barayin man fetur a Neja Delta

DAKARUN Dake aikin samar da Tsaro a Yankin Niger Delta, dake Nigeria, sun yi nasarar kama barayin man fetur 46, da wani jirgin ruwa.Kakakin dakarun, Kanar Timothy Anthiga, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana Gidan Radiyon Faransa cewa, "I ina tabbatar maka, a ranar 20 ga wata, dakarun mu a karamar hukumar Brass dake Jihar Bayelsa, sun yi nasarar kama wani jirgin ruwa da wasu kwale kwale 13, yayin da ake shirin yiwa jirgin lodin mai. Mun kama mutane 46 dake da hannu wajen wannan aika aikan, kuma da zaran mun kamala bincike, za’a gurfanar da su a gaban kotu". 

Babban Ofishin NNPC da ke Abuja, Nigeria
Babban Ofishin NNPC da ke Abuja, Nigeria Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.