Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar :tsohon shugaban kasar na ci gaba da zama a kurkuku.

A yau ma, bayan da aka yi maganar sako Mahamadou Tandja tsohon shugaban kasar Nijar daga gidan kaso,sai gashi bai hito ba.Lauya Souley Oumarou, shi ne ke kare tsohon shgaban kasar ta Nijar,ya furuta cewa,kotu za ta sake diba maganar sakin talala da a kama tsohon shugaban .A dai ranar 10 ga wanan wata ne, ake sa ran kotu za ta diba maganar ta sakin talala ga tsohon shugaban Mamadou Tandja da ake tuhuma da lakume kudin kasar da yawansu ya kai milyar 4 na dalar sefa kimanin Yiro sama da milyon 6.Bugu da kari ana tuhumar tsohon shugaban da kin amuncewa da hukumcin kotun mulkin kasa tare da gudanar da tazarce abun da ya bashi damar kassancewa kan kujerar mulki.Sojin da su ka gudanar da juyin mulki, sun gabatar da wani sakamakon bincike da ya nuna cewa shugaban ya kashe kudin da yawansu ya kai milyar 86 na sefa ,kimanin milyon 129 na Yiro.  

Tsohon shugaban Nijar Mamadou Tandja
Tsohon shugaban Nijar Mamadou Tandja AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.