Isa ga babban shafi
Najeriya-PDP

Jam’iyar PDP ta amince da takarar shugaba Goodluck Jonathan

Jam’iyar PDP a Nigeria, ta amince da takarar shugaba Goodluck Jonathan, a zaben shekarar mai zuwa, da kuma cigaba da karba karba a cikin kudin tsarin mulkin ta.Shugaban Jam’iyar, Dr Okwesileze Nwodo ya sanar da haka, bayan taron Jam’iyar Abuja, abinda ya kawo karshen kace nacen da ya biyo bayan, kiraye kirayen da akewa shugaba Jonathan da ya shiga takara.Wasu daga cikin Yan Arewacin kasar, sun bukaci cigaba da karba karba, dan ganin shugabancin kasar ya zauna a Yankin, a zabe mai zuwa, yayin da wasu ke cewa, tunda shugaba Jonathan da marigayi Umaru Musa Yar’adua tikiti daya ne ya kawo su, yana da kyau ya cigaba har shekara ta 2015.Tuni wannan matsala ta PDP ta mamaye siyasar Nigeria, inda ake ta tafka mahawara kan barin duk wani Dan takara daga kowacce shiya, ya shiga a dama da shi a zabe mai zuwa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.Da wannan mataki, ana saran shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana takararsa, inda ake saran zai fafata da Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. 

Jam’iyar PDP
Jam’iyar PDP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.