Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Jamiyyar PDP Mai Mulki Na Kotu

Shugaban Jam’iyyar dake mulki a Najeriya, PDP. Cif Vincent Ogunlafor ya gurfana gaban wata kotu abirnin Abuja yau inda ake zarginsa da cin hanci da rashawa.Wannan zargi na zuwa mako daya da hawa kujeran Shugabanci da Goodluck Jonathan yayi kuma ya kasance saura shekara shekara daya  ayi sabon zaben Shugaban kasa.Cif Ogunlafor na fuskatar tuhuma ce na karban cin hanci na kudin Najeriya Naira Miliyan 223, alokacin da yake rike da mukamin Ministan Ayyukan musamman karkashin Gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.Cif Vincent Ogunlafor da wasu mutane 3 da ake tuhuma sun karbi hancin tare, sun musanta zargi 14 da Hukumar yaki da Cin hanci mai zaman kanta dake Najeriya ta shigar ICPC.Lauyan Hukumar Adegboyega Awomolo ya fadawa kotun cewa mutun na biyar da ya kamata a hada dasu ya mutu.Alkalin Kotun dake Abuja Ishaq Bello ya bada belin mutanen hudu , inda ya bukace su dasu sake zuwa kotu ranar 21 ga watan gobe saboda sauraron karar. 

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.