Isa ga babban shafi

Twitter ya rufe dinbim shafukan masu yada labaran karya

A yau Juma’a dandalin sadarwa na Twitter ya ce ya rufe dubban shafuka da ke yada labaran karya tare da watsa farfagandan gwamnatoci a wurare kamar Hadaddiyar Daular Larabawa, China da Spain.

Facebook da Twitter sun sha alwashin yaki da yadalabaran karya ta kafensu
Facebook da Twitter sun sha alwashin yaki da yadalabaran karya ta kafensu NICOLAS ASFOURI, Lionel BONAVENTURE / AFP
Talla

Kamfanin ya ce ya rufe shafuka daga China, wadanda ke neman gwara kan masu zanga – zanga a Hong Kong, da kuma wasu daga Masar, da ke aikewa da sakon nuna goyon baya ga Saudiyya da kuma da dama a Hadaddiyar Daular Larabawa da ke aikewa da sako Qatar da Yemen.

Kamfanin ya kuma dakatar da wasu shafuka masu yada labaran karya a Spain da Ecuador.

Wannan bayanin da kamfanin na Twitter ya fito da shi na daga cikin hobbasar da ya ke yi, wajen habakar fahimta kan yadda gwamnatoci ke amfani da farfajiyarsa don jirkita ra’ayin al’umma.

Twitter ya ce ya gano shafuka sama da dubu 4 da dari 3 a da ke kokarin ganin an tada husuma a Hong Kong musamman tsakanin masu zanga – zanga.

Wannan matakin ya biyo bayan rufe wasu shafuka a Masar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Facebook ya yi a watan jiya ne, sakamakon wallafa bayanan da ba su da tushe kan rikice – rikicen Libiya, Sudan da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.