An aikata laifin farko a sararin samaniyar duniya
Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA na gudanar da bahasi kan wani babban laifi da ake kallo a matsayin irinsa na farko da aka aikata a can sararin subhana.
Wallafawa ranar:
Hukumar NASA na tuhumar Anne Mclain bisa zargin ta da kutsawa cikin asusun bankin wata abokiyar zaman madigonta da suka rabu, wato Summer Worden wadda ta shigar da kara domin bi mata kadi.
Mclain ta aikata laifin da ake zargin ta da shi ne a yayinda take aikin watanni shida a can sararin samaniya kamar yadda Jaridar Times ta rawaito.
Worden ta ce, Mclain ta yi mata kutsen asusun ne ba tare da izininta ba, inda take ganin ko kadan ba ta da hurumin sanin abinda asusun ya kunsa lura da cewa, tun a bara ne auren jinsinsu ya mutu.
Sai dai a kokarin kare kanta, Mclain ta ce, ta kutsa cikin asuusn ne domin sanya ido kan kudaden da suka tara tare a lokacin da suke zaman auren jinsi guda, sannan kuma ta tabbatar cewa, kudaden za su isa wajen kula da yaron da suke reno, yayinda ta musanta aikata ba daidai ba.
Tuni dai Mclain ta dawo doron kasar duniya daga sararin samaniyar, yayinda masu bincike suka fara yi mata tambayoyi kan laifin da ake zargin ta da aikata.
Muddin dai aka samu Mclain da laifi, hakan zai kasance laifi na farko da aka aikata a can sararin samaniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu