Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami
Koriya ta Kudu ta ce, Koriya ta Arewa ta sake gwajin wasu makamai biyu masu linzami da suka yi tafiyar kilomita kusan 250 a sararin samaniya kafin fadawa cikin teku.
Wallafawa ranar:
Babban Hafsan Sojin Koriya ta Kudu ya ce, an harba makaman ne daga yankin Wonsan da ke Gabashin gabar ruwan kasar, inda ya ce, wadannan gwaje- gwaje ba za su taimaka wajen samun zaman lafiya a yankin ba.
Koriya ta Arewa ta ce, gwajin wani gargadi ne kan shirin atisayen soji da Koriya ta Kudu da Amurka ke shirin yi a Yankin.
A karkashin wani kuduri, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya haramta wa Koriya ta Arewa gwajin makamai masu linzami, amma sau biyu kenan da kasar ta yi gwaje-gwajen makaman a cikin kasa da mako guda duk kuwa da ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasar da takwaransa na Amurka, Donald Trump a watan jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu