Isa ga babban shafi
Afghanistan, ICC

ICC ta yi watsi da binciken laifukan yaki a Afghanistan

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC, ta yi watsi da yunkurin fara gudanar da bincike game da zargin aikata laifukan yaki a Afghanistan, matakin da ke zuwa bayan Amurka ta soke Bizar babbar mai shigar da kara a kotun, wato Fatou Bensouda.

Babbar Mai Shigar da kara a kotun duniya,  Fatou Bensouda
Babbar Mai Shigar da kara a kotun duniya, Fatou Bensouda ©ICC-CPI
Talla

Tuni kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi tir da matakin da alkalan kotun suka dauka na fatali da bukatar da Bensouda ta gabatar domin fara gudanar da binciken.

Matakin kotun na nufin cewa, a halin yanzu, Kungiyar Taliban da Gwamnatin Afghanistan har ma da Amurka, duk sun tsallake wata tuhuma a kotun na ICC.

Alkalan sun ce, rashin tattara hujjoji tun da farko da kuma rashin hadin-kai daga gwamnatocin da lamarin ya shafa, har ma da dimbin kudin da bincike zai lakume, na cikin abubuwan da suka tilasta musu daukar matakin fatali da binciken.

Sai dai Bensouda ta ce, ofishinta zai daukaka kara domin kalubalantar matakin na alkalan kotun duniyar.

A shekarar 2006 ne, masu shigar da kara a kotun na ICC, suka fara bude kwarya-kwaryar bincike kan aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil’adama da aka aikata a shekarar 2003 a Afghanistan.

A shekarar 2017 ne, Bensouda ta bukaci alkalan kotun da su fadada binciken har zuwa kan sojin Amurka, amma ba a takaita shi akan Taliban da sojin Afghanistan kadai ba.

Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta yi barazanar soke Bizar duk wani alkalin kotun da aka samu da hannu wajen binciken sojin na Amurka, yayinda a makon jiya, kasar ta soke Bizar Bensouda, haifarfiyar Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.