Isa ga babban shafi
Duniya

Sojojin Afrika da na Yamma sun fara atisaye a Nijar

A yau litinin za a fara atisayen sojin hadin gwiwa na tsawon kwanaki 11 da zai hada dakarun kasashe 20, takwas daga nahiyar Afirka, a karkashin jagorancin Amurka da ake kira Flintlock a yankin Agadez da ke arewa jamhuriyar Nijar.

Kimanin sojoji dubu 1 da 900 ne ke cikin atisayen na bana
Kimanin sojoji dubu 1 da 900 ne ke cikin atisayen na bana Reuters/路透社
Talla

Babban Kwamandan Rundunar Amurka mai kula da ayyukan soji a Afrika, Janar Marcus Hicks ya ce, dakaru dubu 1 da 900 daga kasashe 8 yankin Sahel da suka hada da Mali da Niger da Mauritania da Chadi da Burkina Faso da Kamaru da Najeriya da kuma Senegal ne ke halartar wannan atisaye.

Kasashen na Afrika za su atisayen ne tare da sauran takwarorinsu na yammacin duniya da suka hada da Belgium da Canada da Denmark da Jamus da Italiya da Netherlands da Norway da Poland da Spain da Birtaniya da kuma Amurka.

Za a kammala atisayen a ranar 20 ga wannan watan na Afrilu kuma hakan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kokarin maagance matsalar ta’addanci a sassan duniya.

Tun dai a shekarar 2005 ne Amurka ta kirkiro wannan atisayen don gudanar da shi a duk shekara, yayin da ake ganin na bana zai banbanta da na baya saboda sabbin tsare-tsare da aka kawo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.