Isa ga babban shafi
Syria

Mutane Da Yawa Sun Kasa Numfashi A Yankin Da Ake Yaki A Syria

A Kasar Syria mutane masu tarin yawa ne aka basu kulawa ta musamman da magunguna cikin gaggawa yankin Ghouta saboda matsalolin rashin iya numfashi a wuraren da ake tafka yaki wanda ya sa  jami'an lafiya  fargaban an yi amfani da makamai masu guba ne.

Wani yaro da yake sume a asibitin  Khan Sheikhun, yankin Idlib na Syria inda ake zaton guba ya shaka.
Wani yaro da yake sume a asibitin Khan Sheikhun, yankin Idlib na Syria inda ake zaton guba ya shaka. rfi
Talla

Kungiyoyin dake sa idanu akan wannan yaki na cewa mutane akalla 60 suka shiga wannan matsala a yankin garuruwan Saqba da Hammuriyeh bayan wani harin Bam da aka kai

Likitoci a wani wajen kulka da mutane da suka jikkata a Gabashin Ghouta sun ce sun baiwa mutane 29 magunguna na alamun sun shaki  guba da aka watsa a inda suke.

Kungiyoyin basu bayyana an sami rasa rai ba ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.