Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Turkiyya da Iran za su ci gaba da kai farmaki Syria

Kasashen Turkiyya da Iran sun amince da matakin majalisar dinkin duniya kan tsagaita wuta a yankin gabashin Ghouta, sai dai Turkiyyan ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan kungiyoyin ta’addanci a Syrian.

Turkiyya na kallon kungiyoyin 'yan tawayen Kurdawa a matsayin 'yan ta'adda, yayinda a bangare guda kuma Iran ke kallonsu a matsayin barazana ga tsaronta.
Turkiyya na kallon kungiyoyin 'yan tawayen Kurdawa a matsayin 'yan ta'adda, yayinda a bangare guda kuma Iran ke kallonsu a matsayin barazana ga tsaronta. BULENT KILIC / AFP
Talla

A bangare guda kuma wata sanarwa da Iran ta fitar, ta ce matakin tsagaita wutar ba zai hana ci gaba da farmakar kan ‘yan ta’addan da ke barazana ga tsaron kasashen ba.

A cewar babban hafson sojin Iran Mohammed Bagheri za su mutunta yarjejeniyar wadda kasashen duniya suka mara mata baya, amma baza su amince da kyale ‘yan ta’addan ba.

A jiya ne dai, Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kada kuri'ar tsagaita wuta a yankin na Syria a dai dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu a luguden wutar da Syria da kawayenta ke yi ya haura mutum 500.

A cewar kasashen Jamus da Faransa tsagaita wutar zai taimaka matuka wajen isar da kayakin agaji da abinci zuwa yankin na gabashin Ghouta da ke da yawan 'yan tawayen.

Turkiyya dai na kallon kungiyoyin 'Yan tawayen kurdawa a matsayin 'Yan ta'adda inda ta ke da fatan murkushe su, yayinda a bangare guda kuma Iran ke kallonsu a matsayin barazana a tsaronta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.